Asabar 28 Maris 2026 - 16:50
Dukkan Ƙungiyoyin Musulmi su Ɗaga Murya Domin Sake Gina Jannatul‑Baqi’a

Hauza/ An gudanar da wata gagarumar zanga‑zanga a birnin Lucknow na ƙasar Indiya a ranar tunawa da rushe makabartar Baƙi’a, inda malamai da al’ummomi daban‑daban suka halarta domin nuna goyon baya ga sake gina wuraren ziyara tsarkaka na Imamai (AS) da Sahabbai (R).

A cewar rahoton sashen fassara na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an gudanar da zanga‑zangar ne domin yin Allah‑wadai da rushe makabartar Baƙi’a da kuma goyon bayan sake gina mazarorin (wuraren ziyara) tsarkaka na Imamai (AS) da Sahabbai, tare da halartar malamai da jama’a masu yawa a birnin Lucknow na Indiya.

Allah‑wadai da manufofin gwamnatin Saudiyya kan rushe Baƙi'a

Masu zanga‑zangar sun yi Allah‑wadai da manufofin gwamnatin Saudiyya kan rushe Baƙi’a, tare da kira da a gaggauta sake gina waɗannan wurare masu tsarki. Masu zanga‑zangar sun yi ta rera taken adawa da gidan Saud, suna bayyana rashin jin daɗinsu, har ma sun ƙone hoton Mohammad Bin Salman, sarkin Saudiyya, domin nuna fushinsu da baƙin cikinsu kan rushe wuraren ibada masu tsarki. A wajen taron an kuma rera taken adawa da Amurka da Isra’ila, yayin da aka zargi wasu shugabannin ƙasashen Musulmi da kasancewa masu biyayya ga waɗannan ƙasashe.

A yayin wannan taro, Hujjatul Islam Wal Muslimin Kalb Jawad Naqvi, babban sakataren Majalisar Malaman Indiya, ya yi jawabi inda ya nuna baƙin ciki cewa duk da cika shekaru ɗari da rushe Baƙi'a, har yanzu ba a ɗauki wani mataki na sake gina waɗannan mazarori ba. Ya ce ya zama wajibi dukkan ƙungiyoyin Musulmi su haɗu domin sake gina Jannatul‑Baƙi’a, amma abin takaici ba a ga wata gagarumar zanga‑zanga daga gare su ba.

Ya ƙara da cewa a Jannatul‑Baqi’a akwai kabarin ‘yar Manzon Allah (SAWA), Sayyida Fatima Zahra (SA), da matan Manzon Allah da kuma wasu daga cikin Sahabbai. Amma shirun da Musulmi suka yi kan rushe waɗannan kaburbura yana nuna irin rashin kishin addini da ake ciki.

Sukar shirun wasu malamai kan laifukan Amurka da Isra’ila

Babban sakataren Majalisar Malaman Indiya ya kuma soki wasu malaman Musulmi da ya kira masu karɓar kuɗin Saudiyya da Amurka. Ya ce: "a yau Amurka da Isra’ila suna kai hari kan Iran tare da goyon bayan wasu ƙasashen Musulmi, amma waɗannan malamai ba su ma iya yin Allah‑wadai ba. Har ma sun yi shiru kan shahadar ‘yan mata marasa laifi a harin Amurka a Minab. Wannan yana nuna raunin tunani da kuma bautarsu.

Ya kuma ƙara da cewa idan Amurka ta sha kaye, gwamnatocin kama‑karya na yankin ma za su rushe, kuma gwamnatocin jama’a masu ‘yanci za su maye gurbinsu.

Shirun shugabannin Larabawa kan hare‑haren Isra’ila da Amurka

Wannan babban malamin Indiya ya kuma yi ishara da shirun da shugabannin Larabawa suka yi kan hare‑haren Isra’ila da Amurka kan Iran, yana mai cewa waɗannan shugabanni ba Musulmi ba ne. Ya ce sun kuma yi shiru kan laifukan da ake aikatawa a Gaza da kisan dubban yara da mata. Ya ƙara da cewa idan Amurka ta sha kaye a yaƙi da Iran, za a ga juyin juya halin jama’a a Saudiyya, Qatar, Jordan da sauran ƙasashen Musulmi.

A ƙarshe ya yi magana kan sake buɗe mashigar Hormuz da Iran ta yi ga Indiya, yana mai cewa wannan nasara ce ga al’ummar Indiya. Ya ce: "gwamnatin Indiya tana tare da Amurka, amma al’ummar Indiya sun goyi bayan Iran, kuma saboda haka Iran ta buɗe mashigar Hormuz ga Indiya. A yau Hindu, Musulmi da ma mabiyan sauran addinai a Indiya sun haɗu waje guda wajen nuna goyon baya ga Iran.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha